Tsoron Kamuwa Da Coronavirus Ya Sanya Ƴan Majalisa Za Su Tafi Hutu

101

Ƴan majalisar dokokin kasar nan na shirin tafiya hutu na mako biyu domin yin riga-kafi ga yaduwar cutar numfashi ta Coronavirus.

Ƴan majalisar wakilai ne suka fara zartar da wani kuduri don tafiya hutun domin bai wa hukumomin majalisar damar tanadar kayan gwaji a majalisar don tantance masu shiga zauruka da ofisoshin majalisar.

A wata sanarwa da majalisar ta fitar, ta bayyana cewa bayan doguwar muhawarar da aka sha a zauren majalisar, ta amince da kudurin.

Wasu daga cikin bukatun kudirin shi ne majalisar za ta kafa kwamiti na musamman wanda zai yi aiki da hukumomin lafiya a kasar domin ganin cewa an yaki cutar a kasar.

Majalisar ta kuma yi kira ga ma’aikatar watsa labarai da al’adu da ta kara wayar da kan jama’a dangane da wannan cuta ta coronavirus.

Hon Abdulrazak Namdas, dan majalisar wakilai ne a kasar kuma ya shaidawa manema labarai cewa majalisar bata fara hutun ba tukuna, sai duka majalisun biyu za su kara zama domin fitar da ranar da za a tafi hutun.

Namdas ya bayyana cewa majalisa wuri ne da ‘yan siyasa da sauran mutane ke tururuwar shiga, amma babu kayan gwajin da za a rinka tantance su.

Ya ce a wannan ne dalili ne ya sa ya kamata a je hutu ko da na mako biyu ne domin kawo wadannan kayayyaki a rinka gwaji ga mutane kafin su shiga.

A makon da ya gabata ne dai aka samu bullar cutar coronavirus a kasar nan bayan ta shafe sama da watanni biyu a wasu kasashe.

Sai dai hukumar dakile bazuwar cututtuka a kasar nan NCDC ta ce gwamnatin tarayya ta shirya gina wurin gwaji da kula da kuma kebe masu cuta a dukkanin jihohin kasar nan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan