Sarki Sanusi Ya Gaza Bayyana A Gaban Hukumar Yaƙi Da Rashawa Ta Jihar Kano

132

Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya gaza bayyana a gaban hukumar yaƙi da rashawa ta jihar Kano.

A jiya ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa da karbar korafe-korafen al’umma ta Kano ta fara wani sabon bincike kan zargin karkatar da kudade da ake yi wa Sarkin na Kano Muhammadu Sanusi II.

Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa hukumar ta aike da takardar gayyata ga Sarkin na Kano da ya bayyana a gabanta yau da misalin karfe goma na safe.

Hukumar dai tana bukatar Sarkin ya bayyana a gabanta yau Alhamis domin amsa tambayoyi kan yadda aka sayar da wasu filaye mallakin masarautar aka kuma karkatar da wasu miliyoyi naira.

Wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta ta ce an gayyaci Sarkin ne bayan tambayoyi ga daya daga manyan ‘yan majalisarsa, wanda ake zargi yana da hannu a badakalar karkatar da kudaden.

Hukumar ta karbar korafe-korafe ta kaddamar da bincike da dama kan masarautar Kano karkashin Sarki Muhammadu Sanusi II da kuma shi kansa Sarkin.

Binciken da hukumar ta yi sun hadar da na zargin yadda aka kashe wasu daruruwan miliyoyi naira wajen biyan kudin waya tun bayan hawan Sarkin Muhammadu Sanusi II karagar mulki, da bincike kan zargin yadda ake sayar da wasu filaye na gandun Sarki ba bisa ka’ida ba, da kuma bincike kan zargin sayar da filayen masarauta a unguwar Darmanawa da karkatar da kudin.

Wasu dai na ganin duka binciken da majalisar da kuma hukumar yaki da cin hanci da rashawa ke yi na da nasaba da siyasa musamman ganin rashin jituwar da ke tsakanin Sarkin na Kano da Gwamna Ganduje.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan