Shekaru 83 Na Olusegun Obasanjo: Me Ka Sani Game Da Shi?

111

Shugaba Olusegun Obasanjo, janaral ɗin sojan Najeriya ne mai ritaya kuma ɗan siyasa, sannan kuma manomi wanda ke da katafariyar gonar kiwon kaji. Ya yi shugabancin Najeriya har karo biyu. Karo na farko a matsayin shugaban soja wanda ya yi daga shekarar 1976 zuwa 1979. Sannan kuma a karo na biyu a matsayin shugaban farar hula daga 1999 har zuwa 2007.

Shugaba Obasanjo mutum ne mai son barkwanci, saboda haka kullum yana cikin wasa da dariya da mutane. Mutum ne mai matuƙar son ci gaban Najeriya. Yana riƙe da muƙaman sarautar Yarabawa masu taken ‘Balogun of the Owu’ da kuma ‘Ekerin Balogun’ na ƙabilar Egba daga cikin dangin Yarabawa.

An haifi janar Obasanjo ranar 5 ga watan Maris na shekarar 1937 a garin Abeokuta na jahar Ogun.

Ya shiga aikin soja a shekarar 1958, inda ya samu horon soji a makarantar sojoji ta Aldershot.

A lokacin yakin basasar Najeriya, janar Obasanjo, ya jagoranci rundunar sojojin ruwa ta 3 wadanda suka kwato Owerri daga hannunun rundunar sojin Biafra, abinda yasa suka mika wuya har aka kawo karshen yakin.

12 Oct 1977, Manhattan, New York, New York, USA — New York: Lt. General Olusegun Obasanjo of Nigeria addressing the United Nations. — Image by © Bettmann/CORBIS

Duk da cewa kai tsaye bai takarawa ba a juyin mulkin da janar Murtala ya jagoranta a shekarar 1975, amma dai dari bisa dari ya goyi bayansa, inda bayanda janar Murtala ya hau kan mulki aka bashi mataimakinsa.

Kundin tsarin mulkin da aka amince da shi a shekarar 1979, ya fito da tsarin shugabanci irin na Amurka wato mai shugaban kasa da mataimakinsa da kuma majalisar dattawa da ta wakilai.

Kuma kan hakane aka gudanar da zabe a wannan shekarar, inda a ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1979, janar Obasanjo ya mika mulki ga Alhaji Shehu Shagari.

Janar Obasanjo ya kasance shugaban soji na farko a Najeriya da ya mika mulki ga fafar hula cikin lumana.

Obasanjo ya tsaya zabe a shekarar 1999 inda ya lashe zaben shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.

Obasanjo ya sauka ne daga kan mulki a shekarar 2007, bayan ya kammala wa’adi biyu a kan karagar mulki.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan