Ta Fito Fili Kan Dalilin Bincikar Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II

165

Hukumar yaƙi da rashawa da karɓar koken jama’a ta jihar Kano ta gudanar da taron manema labarai kan binciken Sarkin Kano Muhammad Sunusi II.

Takardar bayanan taron da shugaban hukumar Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya karantawa manema labarai ranar Alhamis 5 ga watan Maris na 2020, ta bayyana cewa hukumar ta lura da labarai daban-daban daga kamfanin yada labaru waɗanda suke bayani akan gayyatar da tayi wa Sarkin Kano Muhammad Sunusi II zuwa wurinta domin bincike.

Binciken a cewar takardar, ya biyo bayan zargin taka doka ta sashi na 22,23,da na 26 na hukumar yaki da rashawa da karban koken jama’a ta jihar Kano ta shekarar 2008 (wacce aka yiwa kwaskwarima) a bangaren kula da dajin da ake kira GANDUN SARKI.

Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

Alkaluman bincike na farko sun nuna cewa kamfani mai suna “Country With House Ltd ya zamo kamar jagora a wata badakalar sayar da filaye kimanin Hekta 20 akan kudi Naira miliyan 520 a yankin Darmanawa II karkashin dokar mallakar Fili da ake kira CON-RES 2016-503 ba bisa ka’ida ba ga wani kamfani mai suna Messer Family Home Fund Limited a hannun Sarkin Kano.

Ba Za Mu Fasa Binciken Sarkin Kano Sanusi II Ba – Muhyi Magaji

Binciken har ila yau ya nuna cewa wasu kudaden da aka saka a ma’ajiyar bankin masarautar wadan da suka kasance na cinikin da aka yi sun fito ne daga kamfanin da Sarki Sunusi yake da ra’ayi kansa.

Shugaban Hukumar Muhyi Magaji

Binciken ya kara da cewa dukkan cinikayyar filayen da akayi ba bisa ka’ida ba a yankunan Darmanawa, Hotoro da Bubbugaje an yi su ne ta hannun mutanen masarautar guda 3, wadanda suka hada da Shehu Muhammad Dan Kadai (Sarkin Shanu), Sarki Abdullahi Ibrahim (Malaman Kano) da Mustapha Kawu Yahaya (Dan Isan Lapai) wadanda dukkansu sun yi bayanai da suka nuna akwai bukatar Sarkin ya bayyana gaban hukumar domin warware wasu bayanan da aka gagara ganowa.

Daga bisani cikin takardar, Barista Muhuyi yace saboda wadannan bayanai da sauran makamantan su, hukumar tana umartan Sarki Sunusi da ya bayyana a gaban ta ranan Litinin 9 ga watan Maris 2020 da misalin Karfe 11:00 domin amsa tambayoyi.

Turawa Abokai

1 Sako

  1. Wallahi basu da hankali, don idan zan samu goyon bayan jama’ar zamuje ranar by 10:55am my rushe kofa mu hana sarki shiga.

    Wallahi akwai wulakanci da cin fuska

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan