Tottenham Tasha Lugude Har Gida Kuma Ta Fice Agasar F.A

121

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta gamu da fishin kungiyar kwallon kafa ta Norwich City agasar kalu-bale inda tayi sanadiyyar ficewar Tottenham din adaren jiya.

Tottenham ce dai ta fara jefa kwallon farko inda bayan andawo daga hutun rabin lokaci Norwich ta warware kwallon da aka jefamata.

Saida akaje bugun daga kai sai mai tsaron gida akayi waje da kungiyar kwallon kafan ta Tottenham daci 3 da 2 yayin da ‘yan wasan Tottenham guda 3 suka zubar da Fenarti.

Ayanzu dai ta tabbata cewa Tottenham ta shiga sahun kungiyoyin kwallon kafan dasukafi yin rashin nasara awannan akasar Ingila inda ta shiga jerin wasu kungiyoyin kwallon kafan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan