EFCC Da ICPC Za Su Fara Farautar Ma’aikatan N-Power Da Ba Sa Zuwa Aiki

99

Babban Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Samar da Ayyuka da Koya wa Matasa Sana’o’i, Afolabi Imoukhuede ya ce shirin N-Power zai haɗa kai da hukumomin yaƙi da cin hanci don fara farautar ma’aikatan N-Power da ba sa zuwa aiki.

Mista Imoukhuede ya yi wannan magana ne lokacin da yake bayyana fushi bisa samun karin rahotonni dake nuna cewa wasu ma’aikatan N-Power suna ƙaurace wa Wuraren Ayyuka.

Ya bayyana damuwar cewar shirin ya samu rahotonni da yawa game da mutanen da suke ƙaurace wa wuraren aiki ba tare da samun izini ba, ya kuma bayyana cewa irin waɗannan ma’aikata za su fuskanci hukunci.

“Kiraye-kiraye da ƙorafe-ƙorafe suna ƙaruwa, amma bari in tabbatar muku da cewa muna da tawaga ta musamman da za ta yi maganin haka.

“Na faɗa muku cewa shugaban PPA ɗinka shi ne babban mai kula da kai, kuma an ba su iko su aiko mana da rahoton waɗanda suke ƙaurace wa wuraren aiki daga cikin ku ba tare da izini ba.

“Tabbas akwai hukunci ga ko waye kuma ga kowane ɗaya daga cikin ku wanda kawai ya yadda cewa za ka iya ƙaurace wa wajen aiki a duk lokacin da ka so”, in ji Mista Imoukhuede.

Ya ƙara da cewa shirin zai kuma fara farautar ma’aikatan N-Power masu haɗa kai da masu kula da su don ƙaurace wa wuraren aiki.

Mista Imoukhuede ya ce ma’aikatan na N-Power za su iya ajiye aiki bisa raɗin kansu, maimakon su riƙa ƙaurace wa wuraren aiki.

A ta bakinsa, an yi wa ma’aikatan N-Power 5,781 ritayar dole bisa dalilan rashin ɗa’a.

Mista Imoukhuede ya ce kawo yanzu, shirin N-Power ya karɓi buƙatun waɗanda suke son yin murabus har 11,238 a rukunai biyu.

“Mun amince da buƙatun 8,709 saboda sun cika ƙa’idoji sun kuma tabbatar mana; 2,529 har yanzu ba su samu amincewa ba saboda mun kasa samun su ta lambobin wayar da suka ajiye a shafinmu na yin rijista a Intanet.

“A shirin N-Power, za ka koya, za ka yi aiki kuma ka samu kuɗi, idan kuma ba ka yi aiki ba, ba za ka samu wannan alawus ɗin ba, kana sace dukiyar ƙasa ne wadda ta ɗauke ka”, in ji shi.

Mista Imoukhuede ya ce yin murabus bisa raɗin kai yana nufin mutum bai ci amanar kansa ba, bai kuma ci amanar ƙasa ba, sannan kuma ya bada dama sauran ‘yan Najeriya su amfana da shirin.

Ya yi kira ga masu amfana da shirin da koyaushe su riƙa bin hanyoyin da suka dace wajen neman haƙƙoƙinsu idan an fusata su.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan