Hukuma Ta Baiwa Sarkin Kano Wa’adin Bayyana Ranar Litinin

137

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da karbar korafe-korafe ta jihar Kano ta ce tilas Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya bayyana a gabanta don amsa wasu korafe-korafe duk da cewa sarkin bai bayyana ba kamar yadda hukumar ta gayyace shi.


Shugaban hukumar Muhyi Magaji Rimin Gado ne ya tabbatar wa da BBC hakan, inda ya ce tuni suka gayawa lauyoyin sarkin cewa ya bayyana a hukumar ranar Litinin, 9 ga wannan watan.


Sarkin Kanon dai na fuskantar tuhume-tuhume daga bangarorin gwmnati daban-daban ko a jiya Alhamis ma majalisar dokokin jihar ta kaddamar da wani binciken a kan sarkin.


Sai dai kawo yanzu bangaren Sarkin Kanon ba su ce komai ba tukuna.


Barista Muhuyi ya ce sashe na 31 na dokar da ta kafa hukumar ya tanadi duk wanda aka gayyata ya zo da kansa.


Daga nan ne sai shugaban hukumar ya ce idan bayan cikar wa’adin ranar Litinin ba a samu yin hakan ba, “to ka’idojin da doka ta tanada shi za a yi.”

BBC Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan