Lakcarorin Da Ba Su Shiga IPPIS Ba Ba Za Su Samu Albashin Fabrairu Ba- Buhari

106

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa lakcarorin da har yanzu ba su shigar da bayanansu a sabon Tsarin Biyan Albashi na Bai Ɗaya ba, wato IPPIS, ba za su samu albashin watan Fabrairu ba.

Gwamnatin Tarayyar ta kuma bayyana cewa kawo yanzu, kimanin kaso 55% na mambobin Ƙungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU, sun yi rijista da IPPIS.

Ministar Kuɗi, Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Ƙasa, Zainab Ahmed ta bayyana haka a Kano ranar Alhamis yayinda take yi wa manema labarai jawabi a wani taro mai taken 2020 Management Retreat da aka shirya wa daraktocin kuɗaɗe.

“Abin kaico, ka kan gamu da bijirewa a mafiya yawan gyare-gyare da za ka kawo. Mun samu bijirewa daga ASUU a wajen aiwatar da IPPIS, kuma ina farin cikin bada rahoton cewa a ƙalla kaso 55% na mambobin ASUU sun yi rijista, waɗanda ba su yi ba kuma ba za su samu albashin Fabrairu ba”, in ji Misis Ahmed.

Da take jawabi bisa buƙatar tsarin na IPPIS, ta ce tsarin ya taimaka wajen gano ma’aikatan bogi na Gwamnatin Tarayya fiye da 70,000, kuma nan gaba ana fatan tsarin zai kawar da ma’aikatan bogi gaba ɗaya.

“A wajen kakkaɓe ma’aikatan bogi ne saboda kun yi rijista da IPPIS ta hanyar amfani da hoton yatsa, kuma a halin yanzu muna aiki da ofishin Shugaban Ma’aikata don haɗa tsarin ‘IPPIS HR Module’ da yadda ake biyan albashin shi kansa. Zai taimaka mana sosai wajen alkinta tsarin.

“Na san muna da fiye da ma’aikatan bogi 70,000 da muka gano ta wannan hanyar, kuma ina fata za mu zo lokacin da za mu ce ba mu da ma’aikatan bogi”, ta ƙara da haka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan