An Gano Ƙasar Da Mata Su Ka Fi Maza Daɗewa A Duniya

121

Hukumar Kididdiga ta kasar Turkiyya ta bayyana cewar ta kammala shirya rahota a kan mata na shekarar 2019 da ta shirya.

Rahoton ya bayyana cewa kaso 50,2 na jama’ar Turkiyya maza ne yayin da kaso 48,8 kuma mata.

A Turkiyya akwai maza miliyan 41 da dubu 721 da 136 inda ake da mata miliyan 41 da 433 da dubu 861.

Jama’ar kasar na rayuwa matsakaiciya ta shekaru 78,3, maza na rayuwa shekaru 75,6 ina mata suke kai shekaru 81 a raye.

Sakamakon ya nuna mata sun fi maza dadewa a a raye a Turkiyya inda suke da bambancin shekaru 5,4 da mazan kasar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan