Arsenal Zata Sayi Dan Wasan Tsakiya Na Kasar Turkey

107

Dan wasan mai shekarun haihuwa 21 yana buga wasansa ne a matsayinsa na dan wasan tsakiya kuma mai kwazo da hazaka hakan yasa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta shiga neman wannan dan wasa wato Kokcu.

Ayanzu haka yana buga wasansa a kungiyar kwallon kafa ta Feyernood kuma yana taka leda yadda ya kamata musamman yadda yake taimakawa kungiyar kwallon kafan tasa.

Dan wasan mai shekaru 21 a duniya kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta mikawa kungiyar kwallon kafa ta Feyernood yayin £23m.

Ayanzu haka dai kungiyar kwallon kafa ta Arsenal kofi 1 ne ya ragemata wanda take sa ran dauka wato kofin Kalu-bale na kasar Ingila amma duk sauran kwafa-kwafan datake bugawa anyi waje da ita, shima gasar Firimiyan datake bugawa wasan jeka ka ganine.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan