Coronavirus: Saudiyya Ta Sake Buɗe Masallatan Makka Da Madina

200

Saudiyya ta sake buɗe masallatai biyu mafiya tsarki a Musulunci dake Makka da Madina, bayan da ta rufe su don zuba magani da nufin daƙile yaɗuwar sabuwar cutar Coronavirus, Gidan Talabijin na Al Ekhbariya, wanda mallakin gwamnatin ƙasar ne ya bayyana haka ranar Juma’a.

Saudiyya ta kulle masallatan ne ga alhazai ‘yan ƙasashen waje da masu yawon buɗe ido daga wasu ƙasashe 25 don tsayar da yaɗuwar cutar ta Coronavirus.

Ta kuma ce ‘yan ƙasar da mazauna Gulf Cooperation Council, wato ƙasashen Yankin Gulf da suke son shiga ƙasar dole su jira na tsawon kwana 14 bayan dawowa daga wajen yankin.

Saudiyya ta bada rahoton samun ɓullar Coronavirus har sau biyar.

Al Ekhbariya dai ba ta yi bayanin ko za a bar alhazai su dawo masallatan ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan