Bayan Ya Buga Wasa 100 Ya karya Tarihin Wasu ‘Yan Wasa

20

Za a iya cewa Mohammed Salah ya kama da wuta a kungiyar kwallon kafa ta Liverpool inda ya dage sai karairaya tarihi yakeyi a kungiyar kwallon kafa ta Liverpool dake kasar Ingila.

A jiya dan wasa Salah ya buga wasansa na 100 a kungiyar kwallon kafan ta Liverpool kuma ya zamo dan wasan dayafi kowa zura kwallaye a iya wasanni 100 da ‘yan wasan na Liverpool suka cimma a tarihin zuwansu.

Ga jerin sunayen wasu ‘yan wasan da suka jefa wasu adadin kwallaye lokacin da suka cimma buga wasanni 100 a kungiyar kwallon kafa ta Liverpool:

1 Mohammed Salah yaci kwallaye 70.

  1. Fernando Torres yaci kwallaye 63.
  2. Luis Suarez yaci kwallaye 62.
  3. Robee Fowler yaci kwallaye 62.
  4. Michael Owen yaci kwallaye 54.
  5. Sadio Mane yaci kwallaye 50.
Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan