Manchester United Da Manchester City Agasar Ajin Firimiya

123

Ayammacin yau Lahadi za a fafata wasa mai zafi kuma wasan hamayya a gasar ajin Firimiya ta kasar Ingila tsakanin Manchester United da Manchester City.

Wasan da aka yiwa lakabi da wasan hamayya na birnin Manchester wato Manchester Derby kenan.

Manchester City dai har yanzu tana wakiltar kasar Ingila a gasar zakarun nahiyar turai kuma tana matsayi na 2 a gasar ajin Firimiya ta kasar Ingila.

Ita kuwa Manchester United tana wakiltar kasar Ingila a gasar Europa kuma tana kokarin daga ta tsinci kanta a cikin kungiyoyin kwallon kafa guda 4 na saman teburin gasar ta Firimiya domin ta wakilci Ingila a gasar zakarun nahiyar turai a kakar wasa ta 2020 zuwa 2021.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan