Bayan Tsige Sarki Sanusi II Waye Zai Zama Sarkin Kano?

139

A cikin watan Yunin shekarar 2014 ne Sarkin Kano Mai Martaba Muhammadu Sanusi na biyu ya hau kan karagar mulkin Kano, bayan rasuwar Sarki Ado Bayero.


Hawan Sarki Muhammad Sanusi na biyu kan karagar mulkin Kano ya janyo kace-nace, kafin daga bisani kura ta lafa, har ya samu shiga fada, mako guda bayan nada shi.

Shekaru shida akan karagar mulkin masarautar Kano da Sarki Sanusi II ya yi an samu sabani tare da takun saka tsakanin gwamnatin jihar Kano da masarautar Kano, wanda hakan ya haifar da samar da karin masarautu guda 4 a jihar Kano.

Ranar 9 ga watan Maris din shekarar 2020 gwamnatin jihar Kano ta fitar da wata sanarwa da mai taimakawa gwamnan kan harkokin watsa labarai Salihu Tanko ya wallafa ta ce majalisar zartarwar jihar ta Kano ta amince da a sauke sarkin saboda rashin biyayya.

Sakataren gwamnatin jihar ta Kano Alhaji Usman Alhaji ya ce an sauke sarkin Kano ne saboda nuna rashin biyayya ga dokokin jihar Kano.

Abin tambayar waye zai gaji Sarkin Kano Muhammad Sanusi II?

  1. Mai Martaba Sarkin Bichi Aminu Ado Bayero. Ana Ganin Gwamnatin jihar Kano tana da muradi akansa, musamman ganin yadda su ke danyen ganye da gwamnatin jihar Kano da sauran mukarraban fadar gwamnatin Kano.
  1. Nasiru Ado Bayero Chiroman Kano
    Alhaji Nasiru Ado Bayero, wanda shi ne da na uku a jerin yayan mai martaba marigayi Ado Bayero, akwai labarai da su ke zagayawa nan da can da ke bayyana cewa Chiroman na Kano zai maye gurbin Sarki Sanusi II.
  1. Alhaji Abdullahi Abbas
    Alhaji Abdullahi Abbas da yan siyasa su ka dade suna yi masa fatan ya gaji Kakansa wato Sarkin Kano Muhammad Sanusi I, ta hanyar yi masa kirarin Dan Sarki Jikan Sarki kuma Mai jiran Gado. Domin a wasu lokutan ma an jiyo gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da kan sa yana yi masa wannan kirarin.

4. Abbas Sanusi I.  Alhaji Abbas Sanusi wanda shi ne Galadiman Kano kuma mahaifin shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano,  wanda kuma yana cikin yayan Sarki da su ke da shekaru, ya dade yana burin ganin ya zama Sarkin Kano,  wanda har ta kai da ana yi masa kirarin Alhamis Gaf da Juma’a, Asabar Bayan Sati. Har wasu kuma su kan kara da Mama Uwar Sarakuna.  Shi ma ana kallon zai iya maye gurbin Sarki Sanusi II 

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan