Cutar Corona Ta Ɓulla A Jihar Ogun

112

Hukumar yaki da Cututtuka ta kasa (NCDC) ta bayyana cewar an samu mutum n 2 dauke da cutar Corona a jihar Ogun.

Sanarwar da NCDC ta fitar ta shafinta na Twitter ta ce, mutum na 2 da aka samu da cutar ya yi mu’amala da mutum na farko da ya kawo ta daga Italiya, kuma ana ci gaba da tsare su a jihar Ogun.

Hukumar ta sake jaddada kudirinta na ganin an dakile yaduwar cutar tare da magance gaba daya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan