Jami’an Tsaro Sun Yi Wa Fadar Kano Tsinke Tare Da Fitar Da Sanusi

104

Jami’an tsaro ɗauke da manyan makamai sun yi wa Fadar Masarautar Kano tsinke, tare da tsare Sarki Sanusi a harabar fadar.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, SSG, Alhaji Usman Alhaji ya karanta, Gwamna Ganduje ya ce ya sauke Sarki Sanusi ne sakamakon rashin ɗa’a ga tanade-tanaden Dokar Masarautar Kano.

Sarkin, a cewar SSG, ya ƙi halartar tarukan gwamnati da shirye-shirye da take shiryawa ba tare da wata ƙwaƙƙwarar hujja ba, abinda ke nuna cikakkiyar rashin biyayya.

Majiyarmu ta lura da cewa gomman ‘yan sanda da jami’an Civil Defense, NSCDC sun tare ƙofar shiga fadar, ba shiga ba fita.

BBC Hausa kuma jamai’an tsaro sun fitar da Sarki Muhammadu Sunusi II daga Fadar ta Kano, sa’oi bayan da gwamnatin jihar ta sanar da matakin sauke shi daga sarauta.

Kwamishinan Yaɗa Labaran Jihar Kano, Muhammad Garba ya tabbatar wa da BBC batun, inda ya ce sarkin na cikin kariya ba tare da wata muzgunawa ba.

“Sannan za a kai shi garin da zai zame masa mafaka ya ci gaba da rayuwa a can,” a cewar Mista Garba a tattaunarsa da BBC Hausa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan