Babban Burina Shi Ne In Mutu Ina Sarautar Kano – Muhammadu Sanusi II

84

A jiya Talata gwamantin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ta rugujewa tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II babban burin rayuwarsa.

Watanni shida da su ka gabata Muhammadu Sanusi II ya bayyanawa manema labarai cewa babban burin rayuwarsa shi ne ya mutu akan karagar mulkin Kano.

Muhammad Sanusi II ya ce a gurinsa babu matsayin da ya kai Sarautar Kano, domin ba shi da bukatar wani matsayi ko shugabancin da ya wuce Sarautar Kano.

Ya kara da cewa bani da wani muradi ko fatan samun wani mukami fiye da mukamin Sarkin Kano, saboda haka ina addu’ar daga fadar Kano sai dai in wuce zuwa kabarina.

Sai dai a jiya talata 9 ga watan Maris din shekarar 2020, gwamnatin jihar Kano ta fitar da wata sanarwa da mai taimakawa gwamnan kan harkokin watsa labarai Salihu Tanko ya wallafa ta ce majalisar zartarwar jihar ta Kano ta amince da a sauke sarkin saboda rashin biyayya.

Sakataren gwamnatin jihar ta Kano Alhaji Usman Alhaji ya ce an sauke sarkin Kano ne saboda nuna rashin biyayya ga dokokin jihar Kano.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan