Dattawan Kano Sun Bayyana Kaduwarsu Da Matakin Tsige Sarki Sunusi II

75

Kungiyar dattawan Kano mai suna “Advocates For a United Kano” ta bayyana kaduwa gami da mamakin matakin gwamnatin jihar na tsige mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na 2 daga kan karaga.

A jiya litinin 9 ga watan maris na 2020, sakataren gwamnatin Kano Alhaji Usman Alhaji ya bayyana matakin na tsige Sarki Sunusi na 2 bisa tuhumarsa da da wulakanta al’adun al’umma da kuma masarautar da yake jagoranta.

Cikin sanarwar da suka fitar, dattawan na Kano karkashin jagorancin Alhaji Bashir Usman Tofa, sun bukaci daukacin al’ummar jihar da su kaucewa tayar da tashin hankali da sunan adawa da matakin tsige Sarkin, la’akari da cewa babu wanda ya san karshen fitina idan aka yi kuskuren tayar da ita.

Dattawan sun bayyan rungumar abinda ya faru a matsayin kaddara daga Allah mai kowa mai komai.

Daga karshe sanawar ta ce dattawan za su ci gaba da kalubalantar gwamnatin Kano ta fuskar shari’a kan dukkanin matakan da take dauka na ba dai dai ba, ciki kuwa harda dokar bada damar tsige Sarkin da majalisar dokokin jihar Kano ta kada kuri’ar amincewa da ita a wannan litini

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan