Buhari Ne Ya Bayar Da Umarnin Tube Sarki Sanusi II – Rabi’u Kwankwaso

185

Tsohon gwamnan Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya dora alhakin tube Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu kan shugaba Muhammadu Buhari.

Sanata Kwankwaso ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke wata hira da sashen Hausa na gidan radiyon BBC

Jigon adawar, ya ce “shugabannin gwamnati na Kano su da kansu ne ke cewa umarni aka ba su (su tube sarki Sanusi). Shi ya ba su umarni”.

Ya yi zargin cewa sabanin maganganun da makusantan Buhari ke cewa, shugaban ba ya tsoma baki cikin irin wadannan rigingimu, “sai dai musamman mu nan a Kano yadda muke gani (Buhari) yana hargitsa inda yake sa hannu”.

“Shugaba Buhari yana tsoma hannu cikin al’amuran jihar Kano”, in ji Kwankwaso. “Inda ya kamata ya sa hannun sai mu ga ba nan ya sa hannu ba, inda kuma bai kamata ya sa hannu ba, sai mu ga a nan ya sa hannu”.

Tun bayan daga aka cire Sarkin a ranar Litinin, gwamnatin Buhari a hukumance ba ta ce komai ba akan batun. Sai dai a makonnin baya Shugaba Buhari ya ce ba zai haka baki a harkokin cikin gida na jihar Kano ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan