Yau Al’ummar Kano Suna Cikin Farin Ciki – Abdullahi Umar Ganduje

99

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce yau rana ce ta tarihi kuma ta farin ciki a Kano.

Ya bayyana haka ne a yayin bikin mika takardar kama aiki ga sababbin sarakuna a jihar Kano.

Gwamnan ya bayyana cewa yana cikin jin dadi a wannan rana kuma jama’ar Kano gaba dayansu suna cikin farin ciki.

Haka kuma gwamna Ganduje ya bayyana Aminu Ado Bayero a matsayin shugaban majalisar sarakunan jihar Kano.

A halin yanzu Mai Martaba Aminu Ado bayero ne zai rinka jagorancin taron majalisar sarakuna ta jihar Kano inda ake sa ran sarakunan Gaya da Karaye da Bichi da kuma Rano za su rinka halarta.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan