An Kwashe Litattafan Dake Ɗakin Karatu Na Tsohon Sarki Sanusi

149

An kwashe littattafai da jaridu fiye da 40,000 dake ɗakin karatu da tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya gina a Fadar Kano.

A ranar Litinin ne Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano ta sauke Sarki Sanusi.

A wata tattaunawa da ya yi da majiyarmu, Babban Sakataren Sarki Sanusi, Mujtaba Abba ya ce an kai litattafan wani waje mai tsaro a cikin jihar Kano.

“Abinda ya fi damun Maimartaba shi ne makomar litattafansa, ni da ‘yar uwata muka tsaya don mu tabbatar da cewa mun kwashe litattafan duka. Kwana biyu muka yi ba bacci muna kwashe litattafan”, a cewar Mista Abba, wanda ya yi murabus kwanan nan daga muƙamin Falakin Kano.

Ya bayyana cewa kuɗin litattafan zai kai miliyan N200.

“Ni na siyo mafiya yawan litattafan, kuma zan iya faɗa maka cewa a gwari-gwari, za su kai miliyan N200”, in ji shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan