El-Rufa’i Ya Kai Wa Sanusi Ziyara A Awe

69

A ranar Alhamis ne alamomi suka nuna cewa gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ya je ƙaramar hukumar Awe dake jihar Nasarawa don ziyartar Sarkin Kano da aka sauke, Muhammad Sanusi II.

Majiyarmu ta Daily Trust ta gano daga majiyoyin tsaro cewa Gwamna El-Rufa’i ya bar Kaduna ne da safe don ziyartar Sanusi.

Daily Trust ta ce wakilinta bai iya tabbatar da haka ba daga mai ba gwamnan shawara kan kafafen watsa labarai saboda ba a same shi a wayoyinsa ba.

Majiyar ta ce ba zai iya tabbatar da yaushe Gwamna El-Rufa’i zai dawo Kaduna ba.

A jiya ne gwamnan ya naɗa tuɓaɓɓen Sarkin a matsayin ‘Chancellor’ na Jami’ar Jihar Kaduna, KASU.

Wannan muƙamin dai shi ne na biyu da gwamnan na Kaduna ya ba shi a cikin sa’o’i 24.

Muƙamin farko da Gwamna El-Rufa’i ya ba shi ranar Talata shi ne Mataimakin Shugaban Hukumar Bunƙasa Zuba Jari ta Jihar Kaduna, KADIPA.

Wata sanarwa da mai bada shawara na musamman ga Gwamna El-Rufa’i, Muyiwa Adekeye ya sanya wa hannu ta ce tuɓaɓben Sarki Sanusi II ya amince ya yi aiki a matsayin ‘Chancellor’ na KASU kuma Mataiamkin Shugaban KADIPA.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan