Gida Da Waje Ta Tabbata Akan Kungiyar Liverpool

137

Gida da waje ta tabbata akan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool agasar zakarun nahiyar turai wasannin zagaye na 16 da suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta Athletico Madrid.

Inda a daren jiya Liverpool taga bakin dare a filin wasa na Anfield inda aka caskarata daci 3 da 2 bayan sun kwashe kimanin mintina 120 suna gwabzawa da junansu.

Jimilla yanzu dai idan aka hada wasanni guda biyun da kungiyoyin suka fafata a junansu gida da wake Athletico Madrid nadaci 4 Liverpool nadaci 2.

A kakar wasan data gabata kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ce ta zamo zakwra amma yanzu tayi adabo da gasar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan