Ko Me Ya Hana Abdullahi Abbas Halartar Taron Bikin Naɗin Sarkin Kano Da Na Bichi?

207

A jiya laraba gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci bikin mika takardun kama aiki ga Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero wanda aka gabatar a dakin taro na Coronation dake fadar Gwamnatin jiha.

Bikin bayar da takaradar kama mulkin ya samu halartar gwamna jihar Kano da mataimakinsa, Sakataren gwamnatin jiha, kwamishinoni, yan majalisun kasa da na jiha da kuma manyan ƴan siyasa daga ciki da wajen jihar Kano.

Sai dai abin da ya sanya al’ummar jihar Kano ke tambaya akan dalilin rashin ganin fuskar shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano wato Alhaji Abdullahi Abbas.

Abdullahi Abbas da ƴan siyasa da sauran makusantasa ke masa laƙabin ɗan Sarki Jikan Sarki, yana kan gaba-gaba a manyan tarukan da gwamnatin jihar Kano ke shiryawa.

Hakazalika shugaban jam’iyyar ta APC yana daga cikin zuri’ar Sarkin Dabo, kuma ɗan gidan Galadiman Kano ne Abbas Sanusi wanda yana daga cikin wadanda su ka shiga neman Sarautar Kano.

Tun kafin a tsige tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, wasu masu sharhi akan al’amuran siyasar jihar Kano ke tunanin Abdullahi Abbas zai iya ɗarewa karagar Kano, la’akari da yadda Gwamna Ganduje ke masa kirarin Dan Sarki Jikan Sarki… Mai Jiran Gado.

An dai yi Sarautar Kano, inda Aminu Ado Bayero ya zama Sarki na 15 a zuri’ar fulani, shin kowanne gado gwamna Ganduje ya ke yiwa Abdullahi Abbas fata?

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan