Sanusi Ya Maka IGP, Darakta Janar Na SSS Da Sauransu A Kotu

101

Tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya gurfanar da Babban Sifeton ‘Yan Sanda, Darakata Janar na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, SSS, Babban Lauyan Gwamnatin Jihar Kano da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya a kotu bisa abinda ya kira tsare shi ba bisa ka’ida ba bayan sauke shi daga sarautar Kano.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa tawagar lauyoyin Mista Sanusi bisa jagorancin Lateef Fagbemi, SAN, ta shigar da ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/357/2020 ranar Alhamis a gaban Babbar Kotun Tarayya dake Abuja.

Ya roƙi kotun da ta bada umarnin na wucin gadi “a sake shi daga tsarewa ko killacewa da waɗanda ake ƙara suka yi masa, ta kuma dawo wa da wanda ake ƙara haƙƙinsa na mutuntaka, ‘yancin kai, damar shiga jama’a da zirga-zirga a Najeriya (banda jihar Kano) har zuwa lokacin da za a gama sauraron da yanke hukuncin ƙarar asali ta mai ƙara”.

Idan dai za a iya tunawa, bayan an sauke shi daga sarauta ranar Litinin, da farko sai aka kai shi ƙauyen Loko da yake jhar Nasarawa, amma yanayin da ƙauyen yake ciki da kuma gidan da aka kai shi, wanda babu kayayyakin more rayuwa suka tilasta aka sauya masa wajen zama zuwa Awe, a dai jihar ta Nasarawa.

Labarai24 ta kawo rahoton yadda wasu manyan mutane da suka haɗa da Aliko Dangote da Janar Aliyu Gusau suka shiga suka fita wajen ganin an canza wa tsohon sarkin waje.

Tun lokacin da aka raba tsohon sarkin da Kano, an samu kiraye-kiraye daga ƙungiyoyin fararen hula na sauran ‘yan Najeriya dake cewa a ba sarkin ‘yanci.

A ranar Talata Amnesty International ta ga baiken yadda aka hana sarkin zirga-zirga, tana mai yin kira ga hukumomin Najeriya da su girmama haƙƙoƙin ɗan Adam na tsohon Sarki Sanusi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan