Wakilcin Nasir Yahaya; Kwalliya Ta Biya Kuɗin Sabulu – Al’ummar Daura

123

Al’ummar Ƙaramar hukumar Daura a jihar Katsina, sun bayyana gamsuwarsu da irin yadda dan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar a zauren majalisar dokokin jihar Katsina, ya fitar da su kunya ta hanyar samar musu da aiyukan raya ƙasa a fadin ƙaramar hukumar Daura.

Jawabin hakan ya fito daga bakin al’ummar karamar hukumar ta Daura, a lokacin da su ke ganawa da wakilin Labarai24 na jihar Katsina.

Lawal Abba Daura, daya daga cikin shugabannin matasa a karamar hukumar ta Daura ya bayyana irin yadda Nasir Yahaya Daura, ya ke aiyukan raya kasa a dukkanin mazabun da ke Daura.

“Babu shakka babu abin da zamu ce da wakilcin Nasiru Yahaya ya ke yi mana a zauren majalisar dokokin jihar Katsina, domin ya yi abin a yaba kuma ya tabbata wakili nagari”

Ya kara da cewa a shekarar farko da ya yi a zauren majalisar dokokin jihar Katsina ya yi aikin da babu wani dan majalisa da ya yi irinsa a tarihin ƴan majalisun da aka yi a karamar hukumar Daura.

Lawal Abba Daura ya zayyano kadan daga cikin irin aiyukan da Nasir Yahaya ya yi a tsahon shekara daya yana wakiltar al’ummar karamar hukumar Daura.

  • Gina makarantun Islamiyya guda uku a cikin garin Daura.
  • Samar da magunguna tare da kayan aiki irin na zamani a asibitoci.
  • Samar da litattafai da kayan makaranta da kuma kayayyakin koyo da koyarwa a makarantun Furamare.
  • Rabawa dalibai jarrabawar UTME kyauta domin neman gurbin shiga Jami’a da sauran manyan makarantu da ke fadin kasar nan.
  • Rabawa ƴan Kasuwa jari domin bunkasa kasuwanci.
  • Ingantawa tare da samar da tsaftaceccen ruwan sha a fadin karamar hukumar Daura.

A ƙarshe ya yi kira ga al’ummar karamar hukumar Daura da su cigaba da baiwa Nasiru Yahaya goyon baya domin cigaba da amfana da irin wakilcin da ya ke yi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan