Kotu Ta Bada Umarnin A Saki Sanusi Cikin Gaggawa

105

Wata Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta bada umarnin a saki tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II daga garin Awe dake jihar Nasarawa, garin da aka kai shi tun bayan da aka sauke shi daga sarautar Kano, sannan a ba shi damar zuwa ko’ina a Najeriya, banda jihar Kano.

Mai Shari’a Anwuli Chikere ya bada wannan umarni kamar yadda lauyan tsohon Sarki Sanusi, Lateef Fagbemi, SAN ya roƙa a ƙarar da ya shigar a madadinsa.

Alƙalin ya kuma bada umarnin a sanar da waɗanda ake ƙara wannan umarni na sakin tsohon Sarkin na Kano.

Waɗanda ake ƙara su ne Babban Sifeton ‘Yan Sanda, IGP, Muhammad Adamu, Darakta Janar na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, DSS, Yusuf Bichi, Kwamishinan Shar’ia na Jihar Kano, Ibrahim Mukhtar da Ministan Shari’a, AGF, Abubakar Malami, SAN.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan