Sanusi Zai Tafi Legas Bayan Ya Yi Limancin Sallar Juma’a A Awe

131

Tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II zai bar garin Awe na jihar Nasarawa zuwa Legas don haɗuwa da iyalinsa bayan da ya jagoranci Sallar Juma’a a garin na Awe.

Labarai24 ta bada rahoton cewa wata Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta bada umarnin sakin tsohon sarkin daga Awe, garin da aka kai shi tun bayan da aka sauke shi daga sarauta.

Sarki Sanusi ya halarci Sallar Juma’ar ne bisa rakiyar tsohon abokinsa, gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i.

A cewar wani rahoton BBC Hausa, tsohon sarkin ya yi huɗubar a kan muhimmancin karɓar ƙaddara da kuma ƙarfafa imani a yayin musiba.

BBC Hausa ta ce a huɗubar da sarkin ya yi a garin Awe gabanin Sallar Juma’a, ya yi magana a kan imani da ƙaddara dakuma hikimomin Ubangiji wajen shirya abubuwa.

BBC ta ƙara da cewa Sarkin ya janyo ayoyi da hadisai da suke nuna muhimmancin yarda da ƙaddara.

“Duk abin da Allah Ya kaddara wa mutum to lallai akwai alkhairi a cikinsa”, in ji shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan