Waɗanda Suka Yi Garkuwa Da Sanusi Sun Sake Shi- Kwankwaso

119

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce ya yi farin ciki yadda waɗanda suka yi garkuwa da tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II suka yanke shawarar su sake shi.

Mista Kwankwaso ya bayyana haka ne bayan ya haɗu da Sarki Sanusi a Filin Jirgin Saman Ƙasa da Ƙasa na Nnamdi Azikiwe dake Abuja.

“Na yi farin ciki sosai yadda waɗanda suka yi garkuwa da shi, a halin yanzu sun yanke shawarar su sake shi.

“A yanzu ya zama mutum mai ‘yanci, zai tafi Legas, muna farin ciki da haka sosai”, in ji Mista Kwankwaso.

Mista Kwankwaso ne ya naɗa Sarki Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 14 a 2014.

Bayan da aka sauke Sarki Sanusi daga sarauta ranar Litinin da ta gabata, Mista Kwankwaso ya zargi Shugaba Muhammadu Buhari da hannu a ciki.

Amma gwamnatin jihar Kano da Fadar Shugaban Ƙasa sun musanta cewa Shugaba Buhari yana da hannu a cikin al’amarin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan