Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Dakatar Da Mambobinta Guda 5

185

Majalisar dokokin jihar Kano a zamanta na yau litinin ta dakatarda yan majalisun kananan hukomin hukumomi kamar haka;

1_ Gezawa PDP
2_ Kano Municipal PDP
3_ Warawa APC
4_ Tofa/Rimin Gado APC
5_ Kunchi/Tsanyawa APC

Dakatarwar za ta dauki tsawon wata shida ba tareda sun shiga majalisa domin wakiltar alummarsu ba. Majalisar kafin yanke hukuncin, ta zargi yan majalisun da tada rigima daidai lokacinda ake zama kamar yadda aka saba.

Idan ba’a manta ba satin daya gabata hargitsi ya tashi tsakanin yan majalisar a lokacin da mataimakin shugaban majalisar ya tashi domin neman sahalewar yan’uwansa akan karanta rahoton tuhuma da ake yiwa Mai martaba Sarki Muhammad Sanusi II mai murabus, wanda hakance ta fusata wasu daga cikin yan majalisar har zaman ya gagara a wannan rana.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan