Tumbuƙe Rawanin Sarkin Kano Tonawa Arewacin Najeriya Asiri Ne – Dalung

106

Tsohon Ministan Wasanni da Matasa Barista Solomon Dalung, ya ce cire Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da gwamnatin jihar Kano ta yi a makon jiya ya tona asirin Arewa ne, saboda ‘yan arewa na da riko.

Solomon Dalung ya ce a yanzu haka Arewa ba ta da alkibla domin ba ta bin dokokin addinanta gaba daya.

Tsohon ministan ya bayyana haka ne a lokacin da sashen na muryar Amurka ya ke tattaunawa da jama’a akan tumbuke rawanin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da aka yi a makon jiya.

A mkaon jiya ne dai gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta fitar da sanarwar tumbuƙe Muhammadu Sanusi II daga sarautar Kano.

Cikin wata sanarwa da mai taimakawa gwamnan kan harkokin watsa labarai Salihu Tanko ya wallafa ta ce majalisar zartarwar jihar ta Kano ta amince da a sauke sarkin saboda rashin biyayya.


Sakataren gwamnatin jihar ta Kano Alhaji Usman Alhaji ya ce an sauke sarkin Kano ne saboda nuna rashin biyayya ga dokokin jihar Kano.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan