Coronavirus: UAE Ta Rufe Dukkan Wuraren Ibada

104

A ƙoƙarin daƙile yaɗuwar cutar Coronavirus, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, UAE, ta dakatar da yin salla a dukkan wuraren ibada da suka haɗa da masallatai a dukkan faɗin ƙasar tun daga ranar Litinin zuwa tsawon mako huɗu, kamfanin yaɗa labarai na gwamnatin ƙasar, WAM, ya sanar da haka ranar Litinin.

Adadin waɗanda aka tabbatar sun kamu da Coronavirus a UAE sun kai mutum 98 a ranar Lahadi, a cewar Ma’aikatar Lafiya.

Gwamnatin ƙasar dai ta ɗauki matakai da dama don daƙile yaɗuwar Coronavirus, matakan da suka haɗa da dakatar da bada biza, hana jirage daga wasu ƙasashe shigowa, kulle wuraren shaƙatawa, wuraren ajiye motoci, wuraren motsa jiki, wuraren shan barasa, pubs da sinima-sinima.

Gwamnatin ta kuma hana kamfanoni ɗaukar nayin shirya tarukan bukukuwa, ta kuma roƙi jama’a da su ƙaurace wa taruwa a wuri guda indai mutane sun haura 50.

Matakan da UAE ta ɗauka sun yi daidai da waɗanda maƙobtan ƙasashe suka ɗauka don hana yaɗuwar cutar ta Coronavirus, matakan da suka haɗa da hana haɗuwar mutum da mutum.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan