Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Ciyo Bashin Dala $22.7- Minista

125

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirinta na ciyo bashin dala biliyan $22.7, Ministar Kuɗi, Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsaren Ƙasa, Zainab Ahmed ta sanar da haka ranar Litinin.

Ministar ta bayyana haka ne a wani taro mai taken: “2020 International Conference on the Nigerian Commodities Market” da Hukumar Hada-Hadar Hannayen Jari ta Ƙasa, SEC ta shirya a Abuja.

Ta ce an ɗauki matakin dakatar da ciyo bashin ne duba da abubuwan da suke faruwa a da’irar tattalin arziƙin duniya a halin yanzu.

Majiyarmu ta Premium Times ta ce ɓarkewar cutar Coronavirus da aka samu bara ya karya tattalin arziƙin duniya, inda farashin man fetur ya yi faɗuwar da bai taɓa yi ba a cikin shekara huɗu.

Majiyarmu ta ƙara da cewa sakamakon dogara da man fetur da tattalin arziƙin Najeriya ya yi wajen tafiyar da kasafin kuɗi da kuma karyewar farashin man fetur zuwa dala $57 kowace ganga, hakan ya sa ba za a iya yin wasu abubuwa ba da yawa da suke cikin kasafin kuɗin.

Misis Ahmed ta ce gwamnati ba za ta iya ci gaba da ƙoƙarin karɓo bashin ba ko da Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta sahale mata.

“Abubuwan da suke faruwa a halin yanzu ba za su bada damar ciyo wani bashi ba, duk da dai majalisa tana ci gaba da aikinta bisa shirin ciyo bashin.

“Ɓangare ɗaya na majalisa ya kammala aikinsa, ɗayan kuma har yanzu yana aiki. Saboda haka, aiki ne da gaba ɗaya majalisa take da iko da shi. Muna jira”, in ji ta.

Ministar Kuɗi, Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsaren Ƙasa, Zainab Ahmed
Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan