Hotunan Ziyarar Jarumi Adam Zango A Kamfanin Rahama Sadau

227

Jarumar fina-finan Kannywood da Nollywood Rahama Sadau ta saka hotunanta tare da jarumi Adamu Zango a shafinta na fasebuk, inda ta ke bayyana godiyarta tare da addu’ar Allah ya bar zumucin da ke tsakaninsu.

Tuntuni dai Rahama Sadau ta raba kafa a harkar Kanywood inda ta bude wajen ciye-ciye da shaye-shaye a Kaduna mai suna Sadauz’s lounge.

Jarumar wadda fitacciya ce a cikin fina-finan Hausa na kannywood, ta bude wajen ne musamman domin matasa.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da jaruma Rahama Sadau ta rungumi wani jarumi a hoto ba, domin ko a shekarun baya, tauraruwar fina-finan Hausa ta sha suka musamman a kafofin sada zumunta sakamakon rungumar mawakin nan, Classiq da ta yi.

Wannan ya jawo suka matuka ga Rahama Sadau da Kannywood baki daya, inda akasarin jama’a ke nuna cewa abin da ta yi ya saba wa addininta da kuma al’adar Bahaushe.

Wannan ne ya ja har hukumar da ke sa ido kan tace fina-finai ta dakatar da ita duk da cewa wasu sun yi korafi kan cewa wasu ‘yan wasan sun yi abin da ya fi na Rahama, kuma ba a dauki mataki a kansu ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan