Ana Zargin Samun Mutum Na Farko Da Ya Kamu Da Cutar Kurona A Katsina

72

Ma’aikatar lafiya ta jihar Katsina ta sanar da rahoton wani mutum na farko da ake zargin ya kamu da cutar kurona.

Sakataren ma’aikatar lafiya na jihar Dakta Kabir Musptapha, ne ya bayyana hakan a safiyar ranar Laraba.

Dakta Mustapha, ya ce mara lafiyan ya dawo ne daga kasar Malaysia, kuma yana dauke da alamomin cutar kurona ana ci gaba da binciken lafiyansa.

“Ana saran gobe za a fitar da sakamakon gwajegwajen da aka yi wa mara lafiyan, don tabbatar da abin da ke damunsa.” Ma’aikatar lafiyan ta dauki matakin gaggawa tare da Cibiyar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa Kasa [NCDC] don hana yaduwar cutar.
Daily Trust/Amimiya

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan