Naziru Sarkin Waƙa Yayi Murabusa Daga Muƙaminsa

130

Sarkin waƙar tsohon Sarkin Kano Muhammad Sanusi II, Nazir M Ahmad ya yi murabus daga mukaminsa. Cikin wata sanarwa mai dauke da kwanan watan 13 ga watan Maris din da mu ke ciki, Naziru Ahmad ya bayyana ajiye mukamin na sa akan radin kan sa.

Nazir M. Ahmad ya bayyana godiyarsa akan damar da aka ba shi wajen hidimtawa al’umma, haka kuma ya ce zai cigaba da biyayya ga masarautar Kano da jihar Kano baki daya.

Nazir M. Ahmad ya dade yana rerawa tsohon Sarkin Kano wakoki da dama, kuma an dade ana kiransa da Sarkin waka tun kafin tabbatar da Sarautar daga Sarkin Kano.

A cikin watan Disambar shekarar 2018 ne tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya nada Nazir M. Ahmad a matsayin sarkin wakarsa.

Sai dai al’umma sun bayyana cewa wannan sabuwar sarauta ce da ba a ta taba yi ba a masarautar Kano, inda Sarki ne ya ga ya dace a kirkiro da sarautar kuma a ba Nazir M. Ahmad

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan