Coronavirus: Ganduje, Masari, El-Rufa’i Da Sauran Gwamnoni Za Su Kulle Makarantu

87

Gwamnonin Arewa Maso Yammacin Najeriya sun rufe makarantu na tsawon kwana 30 yayinda Coronavirus ke ci gaba da yaɗuwa.
Labarai24 tana bada rahoton cewa yankin Arewa Maso Yammacin Najeriya ya ƙunshi jihohi bakwai ne da suka haɗa da Jigawa, Kano, Kaduna, Katsina, Kebbi, Sokoto da Zamfara .

A halin yanzu, Najeriya tana da waɗanda Coronavirus ta kama fiye da mutum biyar.

Da yake yi wa manema labarai jawabi a ƙarshen wani taron ganawa na gwamnonin yankin suka yi ranar Laraba, gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa Maso Yamma, ya ce an ɗauki wannan matakin ne don daƙile yaɗuwar cutar a yankin.

Gwamna Masari ya ce rufe makarantun zai fara aiki ne daga ranar Litinin, 23 ga Maris, 2020.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan