Maganar Da Shugaban Gasar Laliga Yayi

132

Shugaban gasar Laliga ta kasar Andalos ya bayyana cewar duk da cutar Coronavirus tanaci gaba da yaduwa tofa babu makawa sai an karasa buga gasar.

Gasar ta Laliga dai an bayyana tafiya hutun makonni guda biyu domin ganin yadda za a shawo kan lamarin cutar tunda har tayi sanadiyyar mutuwar wasu mutanen a kasar ta Andalos.

Gasar dai da zarar andawo daga hutun da akaje na makonni guda biyu za a buga wasannin mako na 28 agasar tsakanin kungiyoyin kwallon kafa guda 20.

Hukumar shirya gasar ta bayyana cewar a watan Aprilu za a dawo fafata wannan gasa ta Laliga domin a karasa buga gasar baki dayanta.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan