Coronavirus: Gwamnatin Tarayya Ta Bada Umarnin Rufe Manyan Makarantu

147

Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin rufe manyan makarantu, makarantun sakandire da na firamare a dukkan faɗin ƙasar nan biyo bayan ɓarkewar annobar Coronavirus.

Ma’aikatar Ilimi ta Ƙasa ce ta bada wannan umarni.

A cewar wata sanarwa da Babban Sakataren Ma’aikatar, Sonny Echono ya fitar a madadin Ministan Ilimi, Adamu Adamu Gwamnatin Tarayya ta kuma bada umarnin rufe dukkan Makarantun Haɗaka 104 da ake da su a ƙasar nan.

An ba dukkan makarantun 26 ga Maris don bin wannan umarni.

Mista Adamu ya umarci Shugabannin Makarantun na Haɗaka da su gaggauta kammala jarrabawar zangon karatu na biyu da ake kan yi, su kuma samar da magunguna da dukkan matakan kariya da suka wajaba a lokacin da ɗalibai suke a makarantu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan