Gurbatacciyar Barasa Ta Yi Ajalin Mutane 33 A Ƙasar Iran

8

Mutane 33 ne suka rasa rayukansu sakamakon shan giya mai guba a jihohin Huzistan da Elborz dake kudancin Iran.

Labaran da jaridun Iran suka fitar na cewa mutane 6 sun sake mutu a yankin Huzistan wanda hakan ya kawo adadin wadanda giyar ta kashe zuwa 26, kuma mutane 265 suna kwance a asibiti.

Mai gabatar da kara na Kerej Muhammad Aayari ya bayyana cewar mutane 7 sun mutu a jihar Elborz sakamakon shan giyar mara inganci.

Aayari ya kuma ce bayan samun labarin cewar giya na maganin cutar Corona da wasu mutane suka yi sai suka je suka sha barasar mara inganci.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan