Wasu Tsofaffi Biyu Sun Gudu Daga Gidan Da Ake Kula Da Su Zuwa Wajen Chasu

17

Wasu tsofaffi 2 A kasar Jamus sun gudu daga gidan kula da gajiyayyu da ake kula da su tare da halartar taron kida da rawa na Open Air wanda daya daga cikin wasannin chasu mafiya girma ne a Turai.

Gidan rediyon NDR na Jamus ne ya sanar da cewa, ‘yan sandan sun gano tsaffin mutanen ma’aurata sun gudu daga gidan kula da gajiyayyu sai suka bi bayansu zuwa wajen rawar tare da samunsu cikin nishadi.

Akwai mawaka irin su Judas Priest, Red Hot Chili Peppers da In Flame a wajen chasun inda suka sanya tsofaffin kin komawa gidan gajiyayyun.

Ƴan sanda dole suka hakura tare da komawa da motar tasin da aka aika zuwa wajen daga gidan ajje gajiyayyun.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan