Gasar Olympic Bazata Yiwwu a Shekara Ta 2020 Ba

14

Daya daga cikin mambobin kwamatin shirya gasar guje-guje da tsalle-tsalle daza ayi a birnin Tokyo na kasar Japan wato Dick Pound ya bayyana cewar babu tabbacin cewar za a buga gasar Olympic a 2020.

Daman tuni ake bayar da shawarwari akan cewa ya kamata a daga gasar nan ta Olympic ta bana inda ita kuwa kasar Japan ga bayyana cewar itafa a shirye take domin fara gudanar da wannan gasa.

Yanzu dai ana tunanin sai a shekara ta 2021 za a gudanar da wannan gasa a can kasar ta Japan inda daman tuni kwamatin shirya wannan gasa suka zauna a cikin makonnan sukace zasu tattauna a tsakaninsu domin samun masalaha don ganin an fafata gasar cikin nasara da annashuwa.

Tuni dai kasashe daga nahiyoyin duniyar nan suka sami tikitin buga wannan gasa a aasanni daban-daban na gasar ta Olympic daza ayi inda kasar Japan zata karbi bakuncin gasar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan