Covid-19: Kimanin Mutum 1000 Sun Mutu A Italiya A Kwana Ɗaya

11

Mutum 969 ne suka mutu cikin sa’a 24 a Italiya sakamakon Coronavirus, kuma mace-macen su ne waɗanda suka fi yawa da aka taɓa a ƙasar tun bayan da annobar ta Coronavirus ta ɓulla.

A yanzu dai jimillar waɗanda Coronavirus ta kashe a ƙasar ta Italiya ya kai 9,13

A cewar BBC Hausa, tun da fari dai shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce: ”ƙarancin kayayyakin aiki na yaƙi da cutar” na daga cikin manyan barazanar da ake fama da ita wajen ceto rayuka.

Italiya ce ƙasar da cutar ta fi muni a Turai. Kusan komai ya tsaya cak kuma mutane na ƙunshe a gidajensu kamar yadda aka yi umarni.

Tun da fari a ranar Juma’a, hukumomi sun yi gargaɗin cewa, akwai yiwuwar a ƙara tsawon lokacin matakan hana zirga-zirgar zuwa 3 ga watan Afrilu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan