Super Falcons Ta Kara Samun Matsayi A Duniya Da Afrika

134

Kungiyar kwallon kafan mata ta Super Falcons ta Najeriya ta kara samun matsayi a nahiyar Afrika dama duniya baki daya game da jaddawalin da hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika wato CAF ta fitar hadin gwiwa da hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA.

Duk da kungiyar tayi wasu watanni batare data fafafata wasu wassnni ba inda ayanzu ta dawo matsayi na 1 a nahiyar ta Afrika a fagen iya taka leda.

Idan kuma aka matsa batun na FIFA da kungiyar kwallon kafan matan ta Super Falcons tana matsayi na 39 a duniya inda yanzu ta koma matsayi na 38 a duniya.

Ga jerin wasu kasashen da aka fitar a nahiyar Afrika daga 1 zuwa 5:

  1. Nigeria
  2. Cameroon
  3. South Africa
  4. Ghana
  5. Ivory Coast

Ayanzu dai sai a watan Yuni za a sake fitar da wani sabon jaddawalin tsaiwar kungiyoyin kwallon kafan na mata.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan