Wani Minista Ya Mutu Sakamakon Larurar Numfashi A Jamhuriyar Nijar

84

Wani minista kuma mai bayar da shawara na musamman ga shugaban Jamhuriyar Nijar Issoufou Mahamadou ya rasu a safiyar Asabar, kwanaki kalilan bayan dawowarsa daga jinya a kasashen ketare a daidai lokacin da annobar coronavirus ke addabar duniya.

Ministan mai suna Mahaman Jean-Padennou, wanda ya tsaya takarar shugabancin kasar ta Nijar a zaben 2016, a lokacin rayuwarsa ya kasance makusanci kuma hadimi ga shugaba Issoufou Mahamadou.

Majiyoyi sun ce Jean-Padennou, ya yi fama da rashin lafiya mai nasaba da numfashi a tsawon lokaci, kuma bai wuce kwanaki 10 da komawa Nijar ba, bayan da ya yi jinya a wani asibiti a Turai.

Rasuwarsa na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen duniya da suka hada da kasarsa ta Nijar ke fama da annobar coronavirus wadda ke sarke hanyoyin numfashi, yayin da ta aika mutane kimanin dubu 60 lahira.

Mutane biyar aka tabbatar da rasuwarsu sakamakon wannan cuta a Jamhuriyar Nijar.

Rfi Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan