Liverpool Zata Sayo Danwasan Inter Milan

145

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool kuma zakarun gasar zakarun nahiyar turai ta bayyana sha’awarta ta daukan danwasan kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan wato Marcelo Brozovic.

Liverpool din ta shiga neman wannan danwasane domin karawa kungiyar kwallon kafan karfi wato garambawul kenan duk da cewar har yanzu kungiyar kwallon kafan ta Liverpool tana kan ganiyarta na zane sauran kungiyoyin kwallon kafa.

Tuni Liverpool ta bayyana cewar matukar za a sayarmata da wannan danwasa to babu makawa zata biya kudi kimanin £52m domin dawo dashi kungiyar ya buga kakar wasan ajin Firimiya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan