Wani malamin addinin Muslunci ɗan asalin jihar Kano, Dakta Isma’il Aminu Abdulkadir ya ce ya samu nasarar fassara littafin Sahihul Bukhari zuwa harshen Hausa, a cewar wani rahoto da Freedom Radio ta wallafa.
Malamin, a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ya yi godiya Allah bisa samun ikon kammala wannan aiki, sannan ya ce ya kammala aikin ne a cikin shekaru takwas.
Turawa Abokai