Ilimi Kyauta: Ganduje Zai Mayar Da Almajirai 1,595 Garuruwansu Na Asali

209

Gwamnatin jihar Kano na shirin fara rage yawan almajirai a makarantun Tsangaya.

Tuni an kammala shirye-shiryen fara mayar da almajiran jihohi da ƙananan hukumominsu daban-daban don a haɗa su da iyayensu, a cewar jaridar Intanet ta Solacebase.

Gwamnatin ta ce wannan yana daga wani ɓangare na tabbatar da ɗorewar shirin Ilimi Kyauta Kuma Wajibi da ta ɓullo da shi.

Wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai, Malam Muhammad Garba ya fitar ta yi nuni da cewa tuni an kammala shirye-shirye don mayar da almajirai 432 zuwa ga gwamnatin jihar Katsina a yau Talata.

Sanarwar da Mista Garba ya fitar ranar Litinin ta nuna cewa an ɗauki wannan mataki ne sakamakon rufe makarantun firamare da na sakandire kimannin makonni uku da suka gabata, makarantun na almajirai suka cunkushe inda almajiran suka rasa matsugunai da kuma wajen zuwa.

“Wannan mataki, wanda kuma an ɗauke shi ne bayan neman shawara, ya yi daidai da matakan kariya da ake ɗauka don daƙile yaɗuwar cutar numfashin a jihar nan”, in ji sanarwar.

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar Kano tana tuntuɓar sauran jihohi don ganin yadda za a mayar da almajiran jihohinsu na asali cikin nasara.

A cewar sanarwar, jihohin da za a mayar da almajiran su ne Katsina, mai almajirai 432, Yobe, 63, Kaduna, 198, Jigawa, 663, Bauchi, 101, Zamfara, 01, Gombe, 09, Nasarawa, 10, ita kanta jihar Kano tana da 117, sai Jamhuriyar Nijar, 01,

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan