El-Rufa’i Ya Kama Malami Da Ya Ajiye Mata A Matsayin Almajirai

204

Gwamnatin jihar Kaduna ta kama wani malami, Aliyu Maikwari a Zariya bisa zargin sa da ajiye ‘ya’ya mata a makarantarsa ta Allo, a cewar jaridar Daily Trust.

Gwamnatin jihar ta ce ta kwashe almajirai 327 daga cikin almajirai 500 da suke a gidan da malamin yake ajiye da su.

Kwamishiniyar Walwalar Jama’a ta jihar Kaduna, Hajiya Hafsat Baba ta bayyana haka a yayin wata tattaunawa da manema labarai.

Ta ce daga cikin almajiran da aka kwashe, 17 mata ne ‘yan shekara takwas zuwa 10, kuma suna zaune ne da sauran yara maza a gida ɗaya.

Ta bayyana wannan yanayi a matsayin wanda ya saɓa wa Muslunci, sannan ta zargi iyayen ‘ya’yan matan da ba da ‘ya’yansu ga mutumin da laifi.

“A lokacin da aka faɗa min ban yadda ba har sai da na ga hotuna. An cakuɗa mata da ba su wuce shekara takwas zuwa 10 ba da waɗannan yara. Mun iya kwashe almajirai 327 daga cikin almajirai 500 da suke a gidan. Saboda taurin kansa sai da muka yi amfani da “Operation Yaki” sannan muka iya kama shi.

“Mun kuma fahimci cewa shi yake bada waɗannan mata aure. A halin yanzu ana kan binciken sa a Kaduna”, in ji Misis Baba.

Ta ce an kama malamin ne a matsayin wani ɓangare na aikin da gwamnatin jihar ke yi na kwashe almajirai daga jihar, a kuma mayar da su wajen iyayensu don daƙile yaɗuwar cutar sarƙewar numfashi ta COVID-19.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan