Buhari Ya Yiwa Gwamnatin Jihar Kano Da Masarautar Rano Ta’aziyya

227

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa bisa rashin da aka yi na mai martaba Sarkin Rano Tafida Abubakar Ilah Autan Bawo, tare da miƙa saƙon ta’aziyya ga gwamnatin jihar Kano da al’ummar masarautar Rano bisa wannan babban rashi.

Buhari ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da babban mai taimaka masa akan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar.

Sanarwar ta ƙara da cewa shugaba Buhari ya shiga jerin wadanda su ka taya iyali da al’ummar masarautar Rano ta’aziyyar wannan basarake, wanda ya taka rawa sosai akan cigaban al’umma.

Hakazalika shugaban ƙasar ya bayyana cewa gwamnatin ta yi rashin mai martaba Sarkin Rano, domin kuwa ya rasu a daidai lokacin da gwamnati ke buƙatar hikima da basirar sarakunan gargajiya domin ciyar da ƙasa gaba

A ƙarshe shugaba Buhari ya yi addu’ar Allah ya yiwa Sarkin rahama tare da jan hankalin iyalin marigayi da su yi hakuri bisa wannan rashi, su kuma ɗora akan irin kyawawan aiyukan da ya yi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan